Harin yanar gizo na kara yawa

0
67

Harin yanar gizo yana kara yawa inda aka kaiwa Birtaniya da Rasha hari a ranar Juma’a, yayin da ya zuwa yanzu harin ya shafi kungiyoyi da kanfanoni dubu 100 a kasashe 150.

Daraktan harkokin shari’ar Tarayyar Turai ya ce Birtaniya da Rasha na daga cikin kasashen da harin ya taba sosai a ranar Juma’a.

Yayinda yake magana da gidan talebijan din ITV Rob Weinwright ya ce kawo yanzu irin hare-haren nan sun shafi kanfanoni da kungiyoyi dubu 100 a kasashe 150.

Ya yi gargadin cewa hare-haren za su kara habaka inda ya kara da cewa za a iya yin wani harin a ranar Litinin.

Harin ya rikitar da na’urorin kungiyar kiyon lafiyar Birtaniya NSH inda ya shafi cibiyoyin kiyon lafiya 45 a kasar baki daya.

Weinright ya ce ana ganin ba ‘yan ta’adda ba ne su ke kawo harin, mutanen da aka saba gani yau da kullun ne.

 

Abdulkarim Rabiu

SHARE

LEAVE A REPLY