Hukumar kwallon kafa Jihar Edo ta nada Austin Eguavoen a matsayin jakadan wasannin lig-lig.

0
655

Hukumar kwallon kafa jahar Edo dake yankin kudu maso kudancin Najeriya ta nada tsahon koci kana kuma tsahon kaftin din kungiyar Super Eagles Austin Eguavoen a matsayin jakadan wasanin League na jahar.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta jahar Frank Itaboye ya ce Eguavoen zai kasance abun koyi ga matasan da ke tasowa kana kuma ke sha’awar wasannin kwallon kafa.

Eguavoen wanda yanzu haka ke kasar waje, ya yi alkwarin zama jakada na gari wajan taimaka wa harkokin wasanin kwalon kafa a jahar.

Wannan dai shi ne karon farko da irin hakan ke faruwa a Najeriya. Wanda kuma ana ganin hakan zai rika taimakawa harkokin wasani a matakai daban daban.

 

Abdulkarim/Nura M.

 

 

 

 

SHARE

LEAVE A REPLY