Hukumar kwastam ta fara gwanjon kayayyakin da ta kama

0
8963

Hukumar hana fasakauri ta Najeriya wato Nageria Customs Service (NSC) ta fara gwanjon kayayyakin da ta kama a wurare daban daban na kasar a shafinta na intanet.

Kayayyakin sun hada da wadanda hukumar ta kama da wadanda masu fasakaurin suka tsere su ka bar  su kamar yadda hukumar ta sanar sun jima a hannunta.

Shugaban hukumar kwastam ta Najeriya Kanal Hamid Ali wķkanda ya kaddamar da gwanjon ya ce za a yi gaskiya ta adalci a tsarin cefanar da kayayyakin.

Bisa ga tsarin gwanjon kayayyakin, wadanda suke ta shaidar biyan kudaden haraji daga hukumar tattara haraji ta kasa FIRS ne kadai zasu iya sayan kayayyakin da za cefanar.

Bayan biyan kudin shigar ciniki Naira 1000, wadanda suka cancanci sayan kayayyakin zasu shiga shafin intanet na hukumar domin zabar abin da suke so su saya.

 

Abdulkarim

 

SHARE

LEAVE A REPLY