Hukumomi a Tanzaniya sun bayar da Umarnin tsare wata yar majlisa

0
69

Hukumomi a Tanzaniya sun bayar da Umarnin tsare wata yar majlisa daga jam’iyyar adawa bisa zargin cin zarafin shugaba John Magufuli.

Wannan umarnin na zuwa ne kwanaki kadan bayan da Shugaba Magufuli ya gargadi shugabanin jam’iyyar adawa agame da muggan kalamai kana ya bukaci hukumomin kasar su dauki mataki akan ko wane shugaban jamiyyar adawa wanda yarura wutar rikici.

Kwamishinan Gundumar Kinondoni, Ali Hapi ya umarci yan sanda su tsare Halima Mdee wata yar Majalisa daga Babbar Jamiyyar Adawa ta CHADEMA, dake birnin Dae Es Salaam babban birnin Kasar, kana a tsare ta har tsawon a wannin 48.

Yan adawar dai sun zargi Shugaba Magufuli da rashin iya shugabanci da kuma ci gaba da mulkin kama karya.

Abdulkarim.

SHARE

LEAVE A REPLY