Jihar Neja ta Fara Raba Takin Zamani ga Manoma

Shu'aibu Othaman Sambo

0
259

Gwamnan Jihar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya, Abubakar Sani Bello, ya kaddamar da shirin sayar da takin zamani tan 15,000 ga manoma da kudinsa ya kai Naira Miliyan dubu da dari biyar domin amfanin daminar bana.

Gwamna Sani Bello ya gargadi monaman da su guji sayar da takin da aka saukar da farashin nasa domin samun kazamar riba, domin kuwa duk wanda aka samu da laifin karkatar da takin zai fuskanci fushin hukuma.

Gwamnan ya yi wannan gargadin ne a ranar  alhamis, a wajen bikin kaddamar da sayar da takin zamanin domin amfanin daminar bana.

Takin da za a raba bana dai ya karu da kashi 200 cikin 100 idan aka yi la’akari da yadda aka sayar da takin a shekarar bara.

 

Ga Wakilinmu a Jihar Neja shu’aibu Othman Sambo dauke da Cikakken Rahoto:

REPORT 11 – 05 – 2017 FERTILIZER SALE

 

Abdulkarim Rabiu/SO

SHARE

LEAVE A REPLY