Karamar Hukumar Gumi a Zamfara ta raba Kwalele 15 ga manoma

0
342

Majalisar Karamar Hukumar mulki ta Gummi dake cikin jahar Zamfara ta sayo kwale kwale guda goma sha biyar (15) domin raba su a yankunan dake da gulabe da manyan rafukkan dake cikin yankin.

Shugaban majalisar karamar Hukumar Alhaji Sa’idu Bawa Daki Takwas shine ya bayyana haka a wajen bikin Hannanta kwale kwalen ga mutanen dake cikin karamar Hukumar a makon da ya gabata.

Alhaji sa’idu Bawa ya bayyana cewa majalisar karamar Hukumar ta kashe kudi Naira dubu dari biyu (=N=200,000.00) wajen sayo ko wane kwale kwale daya, kari akan kudin sufarin shi zuwa yankin.

Shugaban ya ce sunyi hakane domin tallafa wa manoma da yan kasuwar dake wasu yankunan karamar hukumar da gulabe suka shingance tsakaninsu da wasu sassan yankin da wasu sassan wannan kasa ta Najeriya.

Ga Rahoton Hamisu danjibga daga Zamfara

 

Abdulkarim/Hamisu Danjibga

 

SHARE

LEAVE A REPLY