Kasar malawi ta bayar da umarnin kama thhohowar shugabar kasar

0
93

Kasar Malawai ta bayar da umarnin kama tsohuwar shugaban kasar Joyce Banda, sakamakon laifukan da ake zarginta da aikata wa, da suka hada da saba ka’idodin aiki da kuma sama da fadi da dukiyar gwamnati yayin da ta ke kan karagal mulki.

Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan kasar, James kadadzera ya ce laifukan da ake zargin tsohowar shugabar kasar ta aikata na daya daga cikin badakalar cin hanci da rashawa da aka bankado a cikin shekara ta 2013, a inda jami’an gwamnatin kasar suka wawure miliyoyin daloli daga baitil malin kasar.

A wata sanarwa, kakakin rundunar ‘yan sandan yace ‘’ shaidun da aka tattara sun isa su bada hujjar zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa tsohowar shugabar kasar’’

 

Abdulkarim

LEAVE A REPLY