kasashen Afrika za su kara maida hankali kan muradan ci gaba mai dorewa

0
68

Hukumar bunkasa tattalin kasashen Afrika (ECA) ta majalisar dinkin duniya, ta bayyana cewa shirin muradun samar da ci gaba mai dorewa da kuma Ajandar sauyi ta Afrika na 2063, za su samar da wata dama ga Nahiyar Afrika ta sake yin amfani da ajandarta ta sauyi a cikin tsarin shirin na samar da ci gaba mai dorewa.

Mai bai wa hukumar shawara ta musamman akan muradan shirin samar da ci gaba mai dorewa, Miss Aida Opoku- Mensah ce ta bayyana hakan a wani babban taro na harkokin siyasa akan muradun ci gaba mai dorewa da ya gudana a birnin New York na Amurka.

Ta ce shirye-shiryen biyu suna da kamanni da juna ta hanyoyi daban-daban, ta kara da cewa kawo yanzu ana ci gaba da kokari wajen alakanta dukkannin shirye-shiryen.

Ka zalika Ms Mensah ta yi kira ga gwamnatocin kasashen Afrika da su bayar da fifiko kan fannonin kididdiga a matsayin abubuwan da za su rika amfani da su wajen tsara manufofinsu.

Abdulkarim

 

 

 

 

SHARE

LEAVE A REPLY