Kasashe 11 ne za su fafata a gasar kwallon badminton ta kasa da kasa a Lagos.

0
102

Hukumar kula da kwallon badminton ta Najeriya (BFN) a ranar Talata ta bayyana cewa yan wasa daga kasashe 11 ne za su fafata a gasar kwallon badminton ta kasa da kasa ta shekara ta 2017 da za a yi a birnin Lagos dake kudancin Najeriya.

Babbar sakatariyar Hukumar, Patience Okon ta bayyana cewa za a gudanar da gasar ne a filin wasa na Teslim Balogun daga ranar 26 zuwa 29 ga watan Yuli.

Okon ta bayyyana sunayen kasashen da za su fafata da suka hada da Najeriya, Sri Lanka, Portugal, Masar, Janhuriyar Benin, Italiya, Ghana, Isra’ila, Uganda, kamaru da Indiya.

 

Abdulkarim

SHARE

LEAVE A REPLY