Korarren babban hafsan sojin Sudan ta Kudu ya koma birnin Juba

0
87
Janar Paul Malong

Korarraren babban hafsan sojin kasar Sudan ta Kudu Janaral Paul Malong ya koma Juba babban birnin kasar kwanaki uku bayan korar sa daga aiki da gwamnatin kasar ta yi.

Kakakin shugaban kasar ya bayyana cewa, an yi amfani da dokar kasa wajen cire Malong tare da maye gurbinsa.

Malong ya bar birnin Juba ba tare da yin bikin mika shugabancin sojojin ga wanda ya maye gurbinsa ba, inda ya kuma tafi zuwa kauyensu na Awiel da ke arewa maso-yammacin kasar.

Yadda Malong ya fita daga Juba a sirrance ba tare da wani biki ba ya sanya damuwa a zukatan ‘yan kasar inda wasu ke tunanin zai yi bore ga gwamnati.

Tsohon Janaral din ya dawo Juba a ranar Lahadin nan.

Gwamnatin Sudan ta Kudu ta ce, an kori Malong ne saboda samun matsaloli game da jagorancinsa a rundunar sojin.

 

 

Abdulkarim Rabiu/TRT

 

 

 

 

 

 

SHARE

LEAVE A REPLY