Kotun ICC ta zargi Afirka ta Kudu da laifin kin kama Al-Bashir a 2015

0
100

Kotun Kasa da Kasa Mai Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ICC a ranar Alhamis din nan ta yanke hukuncin cewa, Afirka ta Kudu ta aikata babban laifi kan kin kama shugaban kasar Sudan Umar Al-Bashir a yayin da ya ziyarci kasar a shekarar 2015.

Kotun ta ce, Afirka ta Kudu ta saba dokar yarjejeniyar Rome da ta sanya hannu a kai.

Kotun da ke birnin Hague na kasar Holan ta ce, yadda Afirka ta Kudu ta ki kama Al-Bashir tare da mika mata shi ya hana ta gudanar da aiyukanta.

Kotun ta ICC ta ce, Umar Al-Bashir ba shi da rigar kariya ta diplomasiyya kamar yadda Afirka ta Kudu ta fada sakamakon yadda ya aikata laifukan yaki da take hakkokin dan adam a yankin Darur na Sudan.

A shekarar 2015 Al-Bashir ya ziyarci kasar Afirka ta Kudu inda ya halarci taron kasashen Afirka kuma a lokacin kotun kasa da kasa ta yi kira da a kama shi.

Amma gwamnatin Afirka ta Kudu ta yi watsi da umarnin na neman hana Al-Bashir barin kasar bayan kammala taron.

 

Abdulkarim/TRT

 

 

 

 

SHARE

LEAVE A REPLY