Kusan Yan Cirani 200 ne Suka Mutu Bayan Kwalelensu Ya Kife a Libya

0
155

Rahotanni sun yi nuni da cewa kimanin ‘yan cirani 200 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon kifewar wasu kwala-kwale guda biyu a tekun Meditaraniya a cikin ranakun kiarshen makon.

Kungiyar Kula da ‘yan gudun Hijira ta kasa da kasa (IOM) a kasar Libya tace an sami nasarar ceto mutane 70 a yankin arewa maso yammacin birnin Zawiya, yayin da daya daga cikinsu  ke cewa 133 sun bace.

Haka kuma wasu 80 sun mutu a ranar asabar bayan da nasu kwale-kwalen ya kife yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Turai dare, a cewar rahoton kanfanin dillancin labarai na ANSA, wanda ya samo labarin daga wani da ya tsari da ransa daga cikin bakin hauren.

Hanyan ruwa tsakanin kasashen Italiya da Libya ita ce aka fi yawan zurga-zurga da safara, kana ita ce wadda ta fi hadari da ‘yanci ranin suka fi amfani da ita zuwa Turai.

Fiye da mutane 6,600 ne aka sami nasarar ceto wa a tsakanin ranakun Juma’a da Lahadin wannan makon da ya gabata.

 

 

Abdulkarim Rabiu.

 

 

 

 

 

SHARE

LEAVE A REPLY