LMC ta tabbatar da kama wadanda ake zargi da cin zarafin alkalin wasa

0
764

Hukumar dake kula da wasannin Lig-lig ta Najeriya LMC ta tabbatar da kama mutane uku dake da hannu wajen cin zarafin jami’an wasanin a wasan da aka buga tsakanin kungiyar Wikki Tourist ta garin Bauchi da  Enugu Rangers a filin wasa na Bauchi.

Tuni dai a cewar mahukunta aka gurfanar da wadanda aka kama a gaban kotu domin amsa tuhuma kan cin zarafin alkalan wasa a lokacin wasannin.

Wadanda  yan sanda suka kama sun hada da Mohammed Isa dan shekaru 35 da Hamisu Muhammed mai shekaru 30  da kuma Yola Ishaya mai shekaru 24.

Hukumar ta LMC ta ce jami’an kungiyar kwalon kafa ta Wikki Tourist na bai wa jami’an tsaron hadin kai a kokarin su na samar da muslaha a lamarin.

 

Abdulkarim/ Nura M.

 

SHARE

LEAVE A REPLY