Majalisar dokoki ta gayyaci Jonathan kan badakalar Malabu

0
131

Majalisar dokokin Najeriya ta aike sammace ga tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan game da bayar da lasisin hakar man fetur da aka bayar kan kudi dalar Amurka biliyan 1 a lokacin yana kan mulki.

Badakalar da ake kira Malabu ta afku a shekarar 2011 lokacin Jonathan na kan mulki inda da fari aka fara ba wa kamfanin Malabu Oil and Gas amma daga baya aka kwace aka ba wa kamfanin Shell kwangilar hakan mai a manyan rijiyoyin man fetur.

Kwamitin majalisar da ke bincikar lamarin ya fitar da sanarwa a ranar Larabar nan cewa, gayyatar Jonathan ya bayar da shaida wani bangare ne na neman adalci ga kowanne bangare saboda sunansa ya fito karara a badakalar.

Mamban kwamitin dan majalisa Razak Atunwa ya ce, ’’Jonathan na kan mulki a matsayin shugaban kasa lokacin da ministoci suka aikata badakalar dala biliyan 1, kuma sunansa ya fito a bayanan aiyukan da aka yi kamar yadda mai gabatar da kara a kasar Italiya ya bayyana.’’

Ya kara da cewa, ana gayyatar Jonathan sakamakon yadda Birtaniya ta soki gwamnatinsa kan yadda ba ta yi aiki don amfanar ‘yan Najeriya ba.

A baya dai Goodluck Jonathan ya musanta cewa, yana da hannu a cikin batun.

 

 

Abdulkarim/TRT

 

 

LEAVE A REPLY