Majalisar dokokin Najeriya za ta yi doka kan sauyin yanayi

0
87
Majalisar dokokin Najeriya

Majalisar dokokin Najeriya ce ta tabbatar wa da ‘yanNajeriya cewa za ta fitar da dokar da za ta bai wa majalisar damar duba dalilan da ke janyo sauyin yanayi a kasar.

Shugaban kwamatin majalisar a kan dumamar yanayi Mista Sam Onuigbo daga jahar Abia, shi ne ya bada tabbacin a Abuja babban birnin kasar a yayin wani bikin kaddamar da sabon shirin tinkarar matsalar dumamar yanayi mai taken Glob Najeriya.

Mista Onuigbo yace dokar za ta tabbatar cewa tsare-tsaren gwamnati gami da ayyukanta sun gudana cikin kyakkyawan tsari tare da la’akari da yanayi.

A nasa bangaren jagoran shirin na Glob Nigeria, Sanata Bukar Abba Ibrahim cewa ya yi sabon tsarin zai saukake yadda ake shirya kasafin kudi domin magance kalubalen sauyin yanayi.

 

 

Abdulkarim/Ilyas

LEAVE A REPLY