Malaman Firamare sun sami karin girma a Jihar Katsina

0
1937

Gwamnatin jahar Katsina ta yi karin girma na shekara uku ga malaman makarantun firamare da ke fadin jahar.

Gwamnan jahar katsina Aminu Bello Masari ne ya sanar da hakan a wajen wani bikin yaye dalibai da bayar da kyaututtuka wanda ya gudana a firamaren Ida da ke birnin katsina jahar katsina arewa maso yammacin Najeriya.

Gwamna Masari wanda ya samu wakilcin shugaban hukumar Ilmin bai daya (SUBEB) ta jahar, Malam Lawal Duhari Daura ya bayyana cewa Karin girman ga malaman wani bangare ne na basu kwarin gwiwa domin su rubanya kwazons.

Yana mai cewa ‘’gwamnatin jahar mai ci yanzu ta gaji da bashin Karin girman malaman tun daga na shekara ta dubu biyu da goma sha biyu wada ta gada daga gwamnatin da ta gabata’’.

Lawal Buhari Daura ya kuma bayyana cewa gwamnatin jahar na bada dukkanin gudummuwar da ta dace ga ci gaban ilmin bai daya, inda ya ce kimanin Naira miliyan dari takwas ne gwamnatin jahar ta bayar domin karbo kudaden aiyuka na shekarar dubu biyu da goma sha biyu da kuma fiye da Naira miliyan dubu daya na shekarar da ta gabata ga hukumar tarayya ta Ilmin bai daya.

Wakilinmu dake jahar katsina kamilu lawal na dauke da cikakken rahoton.

Abdulkarim/Kamilu Lawal

 

 

 

 

 

 

Gwamnatocin jahohin Arewa maso

SHARE

LEAVE A REPLY