Manyan hafohin sojin Najeriya sun isa birnin Maiduguri

0
466

Manyan hafohin rundunar sojin Najeriya sun isa birnin Maiduguri a jihar Borno, arewa maso gabashin kasar biyo bayan umarnin mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbanjo cewar manyan sojojin su koma yankin da ya sha fama da hare haren yan ta’addan Boko Haram tare da yin garkuwa da mutanen yankin.

Mukaddashin shugaban kasar ya bada wannan umarni ne domin tabbatar da ganin an maido da zaman lafiya a wannan yanki.

Manyan sojojin sun gudanar da wata tattaunawar sirri tsakaninsu na ganin yadda za a lalubo bakin zaren da kuma kawo karshen irin wannan matsala na ta’addanci baki daya.

Bayan kwashe tsawon awa hudu ana tattaunawa tsakanin manyan hafsoshin sojan kasar karkashin jagorancin hafsan hafsoshin sojojin Najeriya Janar Ilorin Shekin, sai mai magana da yawun rundunar sojojin Najeriya Manjo Janar John Anache ya yi wa manema labarai bayani game da ziyararsu da kuma abin da suka sa a gaba.

Daraktan hulda da jama’a na rundunar sojan kasar Birgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka, yace har yanzu rundunar sojojin Najeriya tana kan bakanta bisa wannan aiki kuma suna neman hadin kai da goyon bayan jama’a musamman wurin basu bayanai da zau taimaka, kamar yadda suke zaton akwai Boko Haram na zaune tare jama’a, don haka kowa ya sa ido kuma ya kai labari ga jami’an tsaro idan ya gano irin wadannan mutane.

 

Abdulkarim/VOA

 

 

 

LEAVE A REPLY