Miliyoyin ‘yan Najeriya nawa Buhari fata da addu’ar samun lafiya

0
133

Tun bayan da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana sake fitarsa zuwa birnin Landan a ranar 7 ga watan Mayu domin dubu lafiyarsa miliyoyin ‘yan Najeriya suka rinka yi masa addu’a da fatan samun lafiya.

Kamar yadda mai magana da yawun shugaba Buhari, Femi Adesina ya bayyana a shafinsa na twitter a ranar lahadin 7 ga watan Mayu, shugaba Buhari ya isa Landan ne domin duba lafiyarsa kuma lokacin dawowarsa zai ta’allakane ga ra’ayoyin likitocinsa. Saboda haka babu wani abin damuwa ko zargi game da dadewar shugaban a birnin Landan.

Kafin fitarsa daga Najeriya, Shugaba Buhari ya aika wasikar sanarwa zuwa ga Majalisun dokokin kasar guda biyu kamar dai yadda kundin tsarin mulkin kasar sashi na 145 (1) ya bada dama.

Bugu da kari shugaba Buhari ya mika ragamar mulkin kasar ga mataimakinsa a matsayin mukkadashin shugaban kasar, a iyakacin kwanakin da zaiyi kafin dawowarsa. Mukkadashin shugaban kasar Professa Yemi Osibanjo ya ci gaba da jan ragamar mulkin kasar cikin tsanaki da daidaito. A ranar litinin 12 ga watan Yuni 2017 mukkadashin shugaban kasar ya sa hannu a kasafin kudin kasar.

Kawo yanzu ‘yan Najeriya da dama na nuna fatansu ga samun lafiyar shugaba Buhari ta shafukar sada zumunta, a yayin da suke addu’oi har ga shafukan facebook na shugaban mai taken President Muhammdu Buhari.

 

 

Abdulkarim/TRT

LEAVE A REPLY