Mukaddashin shugaban Najeriya Osinbajo ya gana da shugaba Buhari a London

0
386

Mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya gana da shugaba Muhammadu Buhari a birnin London wanda ya kwashe fiye da wata biyu yana jinya a can.

Wata sanarwa da kakakin farfesa Osinbajo, Laolu Akande ya wallafa a shafinsa na Twitter, a daren Talata, ta ce “Nan ba da jimawa ba za mu sanar da jama’a yadda ganawa tsakanin shugabannin biyu ta kaya.”

Sai dai ya kara da cewa, “shugabannin biyu sun yi kyakkyawar ganawa.”

Daman dai Laolu Akande ya sanar a daren Talata a shafin nasa na twitter cewa, “Mukaddashin Shugaba Osinbajo zai gana da Shugaba Buhari a London a ranar Talata, sannan zai dawo Abuja da zarar sun kammala ganawa”.

Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa Shugaba Buhari ne ya bukaci mukaddashin shugaban kasar ya je wurinsa domin su tattauna kan wasu batutuwa.

Wannan dai shi ne karo na farko da mutanen biyu za su gana tun da shugaban na Najeriya ya fice daga kasar.

 

Abdulkarim Rabiu

 

LEAVE A REPLY