Mukaddashin shugaban Najeriya, ya yi nadin sabbin sakatarori

0
86

Mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, ya amince da nadin sabbin manyan sakatarori guda 21 a kasar.

Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Winfred Oyo-Ita ce ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da daraktan harkokin sadarwa a ofishinta, Haruna Imrana ya fitar ranar Alhamis.

An zabo sabbin manyan sakatarorin ne daga cikin ma’aikata 300 da suka rubuta jarrabawa don samun wannan mukami.

Sanarwar ta ce sai nan gaba, za a bayyana ma’aikatun da aka tura sabbin manyan sakatarori don fara aiki.

Ma’aikata 300 ne daga hukumomi da sashe-sashe da kuma ma’aikatun gwamnatin tarayya suka rubuta jarrabawa don cike guraben manyan sakatarori a ma’aikatun tarayya.

Ma’aikatan sun fuskanci jarrabawa har mataki uku ciki har da batutuwan tsara manufofi da gudanar da aikin gwamnati da kuma fasahar sadarwar zamani duk a cikin mako daya.

Manyan sakatarorin sun hadar da Mu’azu Abdulkadir da Akpan Sunday da Ibrahim Wen da Adesola Olusade da Anagbobu Nkiruka.

Da kuma Ekaro Chukwumuebobo da Sulaiman Lawal da Aduda Tanimu da Folayan Olaniyi da Nabasu Bako da sauransu.

Abdulkarim/BBC

SHARE

LEAVE A REPLY