Mutane 13 sun mutu kana 175 suka jikkata sakamakon tagwayen girgizar kasa a China.

0
85
Chinese paramilitary police search for survivors after an earthquake in Jiuzhaigou county, Ngawa prefecture, Sichuan province, China August 9, 2017. REUTERS/Stringer

Mutane 13 ne suka mutu sakamakon girgizar kasa mai karfin maki 7 da ta afku a kudu maso-yammacin kasar China.

Haka zalika mutane 175 sun jikkata sakamakon girgizar da ta afku a jihar Sichuan.

Kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya bayyana cewa, a ranar Talatar nan da misalin karfe 9.19 na yamma girgizar ta afku a karkashin kasa da zurfin kilomita 20 a jihar ta Sichuan.

Ana ci gaba da bincike da aiyukan kubutar da jama’a a yankin inda aka tabbatar da gidaje da dama sun ruguje.

A gefe guda kuma yankin Sincan Uygur da ke da nisan kolomita dubu 3 daga Jiujaygou wata girgizar mai karfin maki 6.6 ta afku.

Girgizar ta afku a karkashin kasa da zurfin kilomita 11.

Kasar China na yawan fuskantar matsalar girgizar kasa musamman ma a yankunan kudu maso-yammacin kasa da kuma yankin Uygur mai zaman kansa.

Abdulkarim

SHARE

LEAVE A REPLY