Mutane 21 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a Japan

0
71

Mutane 21 ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a Japan wadda ta afku bayan guguwar Nanmadol ta dagae zuwa kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Kyodo ya bayyana cewa, a makon da ya gabata ne guguwan ta kunna kai zuwa yankin kudu maso-yammacin Japan inda mutane 21 suka mutu.

Mahukuntan sun bayyana cewa, guguwar ta shafi garuruwan Fukuoka, Asakura da Oita inda jami’an ceto ke ci gaba da aiyukan kubutar da mutane wadanda ya zuwa yanzu suka kwashe sama da mutane 700.

Hukumar Kula da Yanayi ta Japan ta ce, za a ci gaba da tafka ruwan sama a yankin kudu maso-yammacin kasar kuma ta gargadi jama’a su kula sakamakon yadda za a iya samun zaftarewar kasa.

Abdulkarim/TRT

 

 

SHARE

LEAVE A REPLY