Mutane 44 ne suka jikkata sakamakon gobara a Masar

0
89

Mutane 44 ne suka jikkata sakamakon kamawar gobara a wata tashar aje man fetur bayan tarwatse wa da wata motar dakon mai ta yi a garin Iskandariyya na Masar.

Kakakin Ma’aikatar Lafiya na Masar Khalid Mujahid ya bayyana cewa, motar da ta fashe na tafiya a kan hanyar Iskandariyya-Alkahira inda kuma mutane 44 ne suka samu raunuka.

Mujahid ya ce, 6 daga cikin mutanen kaso 60 cikin 100 na jikinsu ya kone inda rayuwarsu ke cikin mawuyacin hali.

Abdulkarim/TRT

SHARE

LEAVE A REPLY