Mutane sama da 700 annobar kwalara ta kashe a Somalia

0
158
Annobar Kwalara a Somaliya

Akalla mutane 11 da suka hada da mata da yara kanana ne suka sake mutuwa sakamakon kamu wa da cutar kwalara inda a yanzu adadin wadanda cutar ta kashe suka kai sama da 700 a kasar.

Wani basaraken gargajiya Sa’ida Mahmud Hassan ya shaida cewa, kauyukan Dalhis, Hidley, Hawani da Hul-Adur ne suka fi fuskantar kamu wa da annobar jnda mutane 11 suka mutu.

Wani likita Dakta Abdulmalik Mustafa ya tabbatar da mutuwar mutanen ga kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, yankunan Somaliya sama da 13 ne ke fama da annobar ta kwalara.

Matsalar fari a kasar Somaliya ce ta janyo rashin samun tsaftataccen ruwansha wanda hakan ya janyo yaduwar cutar.

 

Abdulkarim/TRT

 

SHARE

LEAVE A REPLY