Najeriya: Masu Zuba Jari Za su Sami Tabbacin kyakkyawan Yanayin kasuwanci

0
107
Mukaddashin Shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo

Gwamnatin Najeriya ta bai wa masu zuba jari tabbaci cewar gyaran da kwamtin shugaban kasa mai kula da harkokin kasuwanci ya yi kwananan, ya samar da kyakkayawan yanayin kasuwanci garesu, ta yadda zai saukaka musu hurdar kasuwanci a Najeriya.

Maitaimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ne ya bayar da wannan tabbacin a wani taron karawa juna sani na kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa da ya gudana a garin Jos fadar gwamnatin Jihar Flato dake yankin a arewa ta tsakiyar Najeriya.

Ya ce batutuwan da suka shafi sabuwar rijistar kasuwanci, da bayar da bashi, da takardar amincewa da kayan da suke samarwa, da izinin shiga kasa da kuma lura da kayayyakin da za su shigo da su cikin kasar, su ne abubuwan da taron ya maida hankali akai.

’’ mun yi kokarin yin nazari a kan bangarori da dama da suke haifar da matsala wajen yin kasuwanci a Najeriya, a lal misali ga wadanda suke so su yi rijistar kamfanoni a da ya kan dauki lokaci mai tsawo amma yanzu an samu ci gaba ta wannan fanni.’’ A cewar  Mataimakin shugaban kasar, ya kara da cewa “a yanzu zaka iya rijistar kasuwanci daban-daban ta hanyar yin amfani da yanar gizo’’.

Ya ce nan da zuwa watan gobe za a bude bangaren rijistar a shafin internet na Hukumar kula da rijistar kamfanoni ta kasa a Najeriya.

 

 

 

Abdulkarim Rabiu.

 

SHARE

LEAVE A REPLY