Najeriya na da damar samar da dubbun kayayyaki

0
232

Mukaddashin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya bayyana cewa kasar na da damar samar da kayayyaki irin mara sa iyaka.

Osinbajo ya bayanna hakan ne a wani taron karawa juna sani da aka shirya wa kana da matsakaitan ‘’yan kawusa a jihar katsina dake arewa maso yammacin Najeriya.

Da yake jawabi a madadin shugaba Muhammadu Buhari, ya ce a lokacin da Shugaban Najeriyar ya gabatar da jawabi kan kasafin kudi na 2017, shugaban yace gwamnatinmu ta maida hankali akan samar da duk abin da zamu ci, da kuma abubuwan da zamu yi amfani da su.

Osinbajo yace gwamnatin tarayya ta kaddamar da sabon shirin farfado da tattalin arziki da ci gaba, inda ta samar da damarmakin bunkasa kayayyakin da ake fitar da su daga kasar a maimakon dogaro da wadanda ake shigowa da su.

Har-ila-yau ya yabawa alúmma da gwamnatin Jihar katsina dangane da yadda su zaune cikin lumana duk kuwa da banbancin addini da kabilanci dake tsakaninsu, a inda ya bayyana jihar a matsayin cibiyan hadin kan Najeriya.

 

 

Abdulkarim

SHARE

LEAVE A REPLY