Najeriya ta fara daukan matakan kare annobar Ebola.

0
59

Mukaddashin shugaban Najeriya Yemi Osinajo, ya bayar da umarnin kara tsaurara matakai na kare annobar Ebola a kan iyoyoki domin hana shigowar cutar a Najeriya.

An dai fara daukar matakan ne sakamakon rahotannin da suka yi nuni da barkewar annobar a yankin arewacin Janhuriyar Dimokuradiyyar Kongo.

Ministan Lafiya Farfesa Isaac Adewale, ya ce mukaddashin shugaban kasa ya bayar da wannan umarni ne ranar Laraba a taron majalisar Zartarwa da ya gudana a Fadar shugaban kasa dake Abuja babban birnin kasar.

Adewale wanda ya yi wa manema labarai Karin bayani  ya ce kawo yanzu ana gudanar da ayyukan sa ido sosai a duka kan iyakoki da mutane ke shigowa cikin kasar.

 

Abdulkarim

SHARE

LEAVE A REPLY