Najeriya: za a bai wa kasashe damar shigowa domin yin kasuwanci

0
101
Taron majalisar Zartarwar Najeriya

Majalisar zartarwa ta amince da kafa sabon ofishi da zai rinka kula da hadahadar kasuwanci domin dabbaka shirye-shiryen da gwamnati ke da su kan inganta harkar kasuwanci a Najeriya.

Ministan masanantu da kasuwanci Mista Okechukwu Enelamah ne ya bayyana wa manema labarai hakan jim kadan bayan wata ganawa kan yadda za a baiwa kasashe damar shigowa Najeriya domin gudanar da kasuwancinsu.

Ya kuma kara da cewa, sabon ofishin da za a bai wa wanda ya taba rike matsayin ambasada zai taimaka wa shirin Shugaba Muhammadu Buhari na farfado da tattalin arziki.

Mukaddashin shugaban Najeriya farfesa Yemi Osibanjo ne ya jagoranci taron.

 

 

Abdulkarim/Abubakar

SHARE

LEAVE A REPLY