Nan da Mako Guda Mikel Obi Zai Dawo Murza Leda

0
139

Dan wasan kungiyar Kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles Mikel Obi zai dawo bakin daga bayan kammala murmurewa daga raunin da ya samu.

Dan wasan zai dawo murza leda a kungiyar Kwallon kafa ta kasar Chana Tianjin Teda da yake buga wa wasa, a cawar wata sanarwa da kulub din ya fitar.

” A cikin tsakiyar watan Maris din wannan shekarar da muke ciki ne, kungiyar ta tafi birnin Shanghai domin horas da yanwasa a shirye-shirye na fara gasar Lig, kafin Mikel ya samu rauni, lamarin da yasa tawagar kwallon kafan ta maida hankali akan binciken musabbabin samun raunin nasa ’’. A cewar sanarwar

”da farko dai a ranar 24 ga watan Afrilu kungiyar Kwallon kafan ta tura Mikel Burtaniya domin duba lafiyarsa tare da bashi magani.

‘A ranar 26 kuma likitan da ya duba shi ya tabbar da raunin da yasa samu, kana aka samu nasarar yi masa aiki har guda biyu a ranar 29 ga watan Afrilu, yayin da ake sa ran zai koma fagen daga bayan mako guda.’’

Wannan labari mai dadi ne ga kociyan Najeriya Gernot Rohr, wanda ake sa ran zai kira Mikel Obi a wasan neman shiga gasar cin kofin kasashen Afrika na shekara ta 2019 mai zuwa  da za su kara da kasar Afrika ta Kudu.

 

Abdulkarim Rabiu

 

 

SHARE

LEAVE A REPLY