Rundunar sojin Najeriya ta kaddamar da motocin suntiri da aka kera a kasar

0
245

A ranar litinin din nan ce rundunar Sojin Najeriya ta kaddamar da sabbin motocin sunturi da aka kera a cikin kasar domin bunkasa ayyukan tabbatar da zaman lafiya da dakarun ke yi a daukacin kasar.

Ministan Tsaro Mansur Dan Ali shi ne ya kaddamar da motocin kuma ya aza tubulin ginin wani sabon barikin soji da aka yi wa lakabi da Muhammadu Buhari a kauyen Giri dake kan titin zuwa filin sauka da tashin jiragen sama na Abuja babban birnin kasar.

Shugaban Rundunar sojin kasan Najeriya Janar Tukur Buratai yace rundunar sojin ce ta tsara yadda za a kera motocin a cikin Najeriya bayan ta gudanar da cikakken bincike.

Janar Buratai ya bayyana cewar za a ci gaba da anfani da tsarin a matsayin wani yunkuri na karfafa gwiwar dakarun Najeriya yayin da ake ci gaba da kokarin kakkabe raguwar ‘yan taaddan Boko Haram da suka rage a arewa maso  gabashin kasar.

Yace kawo yanzu an riga an tura wasu daga cikin motocin zuwa yankin arewa maso gabas.

 

Abdulkarim

 

 

 

LEAVE A REPLY