Rundunar sojin Najeriya ta kama yan Boko Haram 126 sansanin yangudun hijira a Borno

0
448

A ranar larabar nan ce rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa ta kama kimanin mutane 126 da ake zargi ‘yan Boko Haram ne a sansanin ‘yan gudun hijira dake garin Damboa a Jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya.

Manjor Janar Lucky Irabo, wanda shi ne ya sanar da hakan yayin zantawarsa da manema Labarai a garin Maiduguri, ya cewa an bankado wadanda ake zargin ne a wani aikin sunturi da dakarun Najeriyar suka gudanar.

Irabor ya ce an gudanar da ayyukan sunturin ne bayan da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai hari a Unguwar Sabon Gari dake karamar Hukumar Damboa dake cikin Jihar.

“a lokacin harin mun yi hasarar sojoji shida da kayayyakin aiki, kana wasu sojojinmu sun jikkata.

“Bayan mummunan harin, mun yi wani sunturi na hadin gwiwa da ya kunshi dakarun 125 na rundunar sojin Najeriya.

“bisa bayanan sirri da muka samu, mun fahimci cewa akwai yiyuwar ‘yan Boko Haram za su kai hari a garin Damboa Kuma da dama daga cikin ‘yan ta’addan sun shiga sansanin yangudun hijira dake garin’’ In Manjo Janar Irabo

 

 

Abdulkarim Rabiu.

LEAVE A REPLY