Sabon kocin mai tsaron gidan Super Eagles ya kama aiki

0
9174

A wani mataki na kawo karshen takaddama a kungiyar Super Eagles ta Najeriya kan batun mai tsaron gida da Kocin kungiyar Gernor Rohr ke kokarin ganin ya yi, yanzun haka sabon mai horas da masu tsaron bayan kungiyar Enrico Pionetti ya fara aiki.

Duk da rashin mai tsaron gida Super Eagles na daya a kungiyar, Rohr ya ce yana da yakinin cewar sabon kocin zai taimaka sosai ga masu tsaron gida.

A baya dai rashin Ikeme wanda shi ne na daya a cikin masu tsaron baya ya sanya kungiyar ta sha kashi a wasan da suka buga da kasar Afrika ta kudu a wasanin neman cancanta zuwa gasar cin kofin nahiyar Afrika inda aka doke Najeriya da ci 2-0.

Sabon Kocin dan shekaru 62 wanda kuma tsohon mai tsaron gidan kasar Italiya ne, ya kuma kamawa kungiyar Lecce  daga shekara ta 1983 zuwa da 86 kana kuma ya kamawa Brescia a shekara ta 1986 zuwa da 87, ya iso Najeriya a ranar Litinin ne domin ya kama aiki.

Abdulkarim/Nura M

LEAVE A REPLY