Sojin Mali 10 sun yi batan dabo sakamakon wani harin kwanton bauna

0
113

Rundunar sojin Mali ta bayyana cewa sojoji goma sun yi batan dabo, biyo bayan wani harin kwanton bauna da wasu da ake zirgin yantawaye ne suka kai a yankin arewacin kasar.

Mai magana da yawun rundunar sojin kasar kanal Diarran Kone, ya ce an kai hari akan jerin gwanon motocin sojojin ne akan titin da ya hada garuruwan Gao da Menako.

Kasashe biyar na Nahiyar Afrika sun kafa wata rundunar soji ta hadin gwiwa domin yakar ayyukan ta’addanci a yankin Sahel, yayin da tashe-tashen hankula ke ci gaba da yaduwa har ma suke kokrin wuce arewacin Mali dake makwafta da kasahen.

A wani labarin kuma a makon da ya gabata ne fada ya kaure tsakanin bangarorin da basa jituwa da juna a kungiyar yantawayen Tuareg, lamarin da ya haifar da zaman dardar a yankin Kidal dake can arewacin kasar.

Abdulkarim

SHARE

LEAVE A REPLY