Super Eagles ta koma sansannin atisaye domin shirin tunkarar wasan cin kofin kalubale na Afrika

0
725

Yanzun haka yan kugiyar Super Eagles dake wasan su a gida sun sake komawa sansanin horas da su dake kanon Dabo domin ci gaba da daukan horo na tunkarar wasanin neman cancanta shiga gasar cin kofin kalubale na nahiyar Afrika a wasan da za su yi da Janhuriyar Benin cikin wannan watan na Agusta.

A makon da ya gabata ne dai mataimakin kocin kungiyar Salisu Yusuf ya sallami wasu daga cikin ‘yan kungiyar domin su bugawa kungiyayinsu wasanin Premier League a wasanni karo na 32 da aka buga a karshen makon da ya gabata.

Yan wasan na Super Eagles za su buga wasa ne da Janhuriyar Benin a ranar 13 ga watan August a Birnin Cotonou, inda kuma bayan mako daya ‘yan kasar ta Benin zasu zo Najeriya inda za’a buga wasan zagaye na biyu a Birnin kanon Dabo a ranar 19 ga wata.

Kasar Benin dai ita ce ta fitar da Togo a wasanin da suka buga inda aka tashi da bugun fenariti da ci 7-6 bayan sun tashi da ci 2-2.

 

Abdulkarim/Nura M.

SHARE

LEAVE A REPLY