Trump ya gana da Shugaba Putin na Rasha a taron G20

0
138

A wannan Juma’ar ce ake haduwar farko ta keke da keke tsakanin shugaba Donald Trump na Amirka da shugaba Vladimir Putin na Rasha a daura da babban taron kasashe 20 masu karfin masana’antu.

A jajibirin wannan haduwa shugaban na Amirka ya furta kalammai tun daga birnin Varsovie inda ya zargi Rasha da nuna halaye na raba kanu, da kuma yin shishigi a zaben shugaban kasar Amirka da ya gudana na 2016.

Sai dai irin zafin da ake sa ran wannan tattaunawa za ta yi tuni ake ganinsa a wajen zauran taron, inda dubban masu zanga-zanga daga sassa daban-daban na duniya suka hallara a birnin na Hamburg domin nuna adawarsu ga taron na G20.

Wata arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami’an tsaro ta yi sanadiyyar jikkatar ‘yan sanda 76.

Shugaban kasar ta Amirka bayan ya nuna yabo ga shugaban Rasha a baya, ya ja da baya kan irin huldar da ya son kullawa da kasar ta Rasha sakamakon tarin zargin da aka yi masa na huldar boye da kasar ta Rasha.

 

Abdulkarim/DW

 

 

 

 

 

SHARE

LEAVE A REPLY