UNICEF: Ana cin zarafin yara dake ketarwa Turai daga Libya

0
56

Asusun tallafawa kananan yara na majilisar dinkin duniya UNICEF ya bayyana cewa a na cin zarafin dubban yara ‘yan Afrika a kasar Libya wadanda suke kokarin ketarawa zuwa Italiya da cikin Tukun Meditaraniya.

UNICEF ya ce galibin yaran Afrika da suke gudun hira ba tare da sanin iyayensu ba, su na yin hakan ne sakamakon cin zarafinsu da ake yi a gida da kuma rigingimun da suka shafi iyali, sannan da yunkurin neman aiki a kasashe dake makwaftaka da Nahiyar Afirika.

Daruruwan ‘yangudun hijira sun bayyana wa Asusun tallafawa kananan yaran na majalisar dinkin duniya cewa, suna fuskantar matsaloli irin na satar mutane domin neman kudin fansa, da kuma kamasu tare da tsare su a gidan yari a kasar Libya, kuma wannan ne yake sa su yi kasadar bi ta cikin tekun Meditaraniya domin ketarawa zuwa nahiyar turai.

Abdulkarim

 

 

 

 

 

 

LEAVE A REPLY