UNICEF ta aika da tallafi zuwa Yamen

0
46

Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya aike da kayan taimako zuwa Yaman wanda tuni suka isa Sanaa babban birnin kasar.

Kakakin UNICEF da ke Yaman Muhammad Al-Asadi ya bayyana wa manema labarai cewa, jiragen dakon kaya 2 da ke dauke da magunguna tan 33 sun isa filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Sanaa.

Asadi ya kara da cewa, za a kai magununan na cutar amai da gudawa zuwa ga yankunan da cutar ta fi tsauri.

Alkaluman Hukumar Lafiya ta Duniya WHO sun bayyana cewa, daga ranar 27 ga watan Afrilu zuwa yau mutane dubu 1,713 ne suka mutu sakamakon cutar ta kwalara.

Sakamakon yakin da aka dauki shekaru 2 ana yi a Yaman kusan mutane miliyan 3 ne suka rasa tsaftataccen ruwan sha.

 

Abdlkarim/TRT

 

 

 

 

 

 

 

 

 

SHARE

LEAVE A REPLY