Wajibi ne ‘yan Najeriya su mallaki katin shaidar ‘dan kasa kafin samun fasgo.

0
114

Hukumar kula da shige da ficen baki ta kasa a Najeriya ta sanar da cewa daga ranar 1 ga watan jannairun 2018 wajibi ne yan Najeriya su mallaki katin shaidar zama dan kasa kafin neman iznin samun fasgo na kasa da kasa.

Kwantrola Janar na hukumar, Muhammed Babandede shi ne ya bayana haka ga manema labarai a fadar shugaban kasa dake Abuja babban birnin kasar.

Kwantrolan wanda ya halarci wani taro a fadar shugaban da kwamitin kula da katin shaidar dan kasa, ya ce an yanke wannan sharawa ne domin tattara bayanai na katin shaidar dan kasa da na fasgo wuri guda.

Abdulkarim

LEAVE A REPLY