Wasu maniyyata aikin Hajjin bana sun kasa cika kudin kujera a Zamfara

0
626

A jahar Zamfara wasu daga cikin maniyyatan da suka soma bada kudin ajiyarsu a Hukumar aikin Hajji ta Jahar a watannin da suka gabata, ya zuwa  yanzu wasu daga cikin su sun kasa kammala biyan kudin kujerar zuwa kasa mai tsarki kamar yadda hukumar aikin Hajji ta Najeriya ta bayyana.

Tabbacin hakan ya fito ne daga bakin kwamishina a hukumar aikin Hajji ta jahar zamfara mai kula da sha’anin yada labarai da kiyon lafiya da da’awa,  Alhaji Sanusi Liman Dan Alhaji a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishin hukumar na jahar dake birnin Gusau.

Alhaji Sanusi Liman Dan Alhaji Ya bayyana cewa, a halin yanzu Hukumar ta karbi mafi yawan bizar maniyyatan da suka kammala biyan kudin kujerar su, yayin da yace suna nan suna ci gaba da karbar sauran kudaden kujerar ga wadanda Allah ya huwace masu domin zuwa kasa mai tsarki a wannan shekara.

Da yake bayani akan mata masu juna biyu da masu matslolin dake kawo musu tarnaki wajen gudanar da aikin hajin a wannan shekara, Alhaji Sanusi ya ce basu hadu da wata matsalar da ta shafi wani maniyyaci ba a halin yanzu.

Akan sha’anin ilmantar da maniyyata aikin hajjin wannan shekara sanin yadda maniyyatan za su gudanar da aikin ibadarsu, kwamishinan ya yi bayani akan irin gudun mawar da malaman Addinin islama suka bayar a karkashin bangaren Da’awa ga maniyyatan dake cikin jahar.

Ga hamisu Danjibaga dauke da cikakken rahoto

Abdulkarim/Hamisu Danjibga

 

SHARE

LEAVE A REPLY