‘Yan adawa sun yi zargin magudi a zaben ‘yan majalisar dokokin Sanagal

0
74

Jam’iyyun adawa a Sanagal sun bayyana cewa, an samu kalubale na rashin bin ka’idoji da kuma yin barazana a yayin zaben ‘yan majalisar dokoki da aka yi a ranar Lahadi a kasar.

Sakamakon da aka fara fitar wa na nuna yadda jam’iyyar shugaban kasar Macy Sall ta ke kan gaba.

Tsohon shugaban kasar Abdullahi Wade ya bayyana cewa, kayan zabe sun isa mazabarsa a makare musamman ma a garin Touba mai tsarki inda sai da ‘yan sanda suka yi aikin kwantar da hankulan mutane da ke zanga-zanga.

Ya ce, an hana jama’arsu samun damar jefa kuri’a su zabi abin da suke so. Abin takaici ne yadda aka lalata demokradiyyar da ya assasa a kasar.

Tashar talabijin ta Walfajir ta nuna yadda wasu mutane suka kai hari kan akwatunan zaben tare da watsar da kuri’u sakamakon kai kayan zabe a makare a garin Diourbel.

 

Abdulkarim/TRT

SHARE

LEAVE A REPLY