Yemen: An sanya dokar ta baci sakamakon barkewar annobar Kwalara

0
65

Rahotanni daga Yaman na cewa, annobar kwalara ta barke a wani gidan Yari da ke hannun ‘yan tawayen Houthi a Sanaa babban birnin kasar.

Wani da aka bayyana sunansa da Abdurrahman Barman ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa, mutane 24 ne annobar ta fara kama wa a gidan kurkukun na Hebra.

An kai mutane 4 daga cikin zuwa asibiti saboda mummunan halin da suke ciki.

Barman ya bayyana musabbabin barkewar cutar da rashin tsaftar gidan yârin.

A makon da ya gabata Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa, mutane 51 cutar kwalara ta kashe a Yaman tun daga watan Afrilu zuwa yau.

Hukumar ta ce, akwai kuma mutane dubu 2,752 da cutar ta kama.

To sai dai kuma an sanya dokar ta baci a Sanaa babban birnin kasar Yemen bayan Barkewar annobar cutar ta kwalara wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

Kawo yanzu dai asibitoci dake birnin cike suke da masu dauke da cutar.

Kungiyar agaji ta kasa da kasa Red Cross ta ce yawan wadanda suka kamu da cutar ya rubayya har sau uku a cikin mako guda inda ya haura fiye da mutane 8,500.

Tuni dai kasar Yemen ke fuskatar matsalar yunwa, da yakin basasa, wanda hakan ya janyo barkewar annobar Kwalara.

 

 

Abdulkarim Rabiu.

SHARE

LEAVE A REPLY