Za a Karrama Tsohon shugaban Najeriya Umaru ‘Yar Adua

0
362

A ranar talata mai zuwa ne Kamfanin Jaridar Daily Trust (DTN) zai karrama marigayi tshohon shugaban Najeriya Umaru Musa ‘Yar Adua da tsohon Manajan daraktan kamfanin DTN, marigayi Alhaji Babatunde Jose (OFR).

Za a bada lambobin yabon ne a wani taron karrama fitattun yan Najeriya da kamfanin Jaridar Daily Trust din zai shirya a daya daga cikin bukukuwan cikarsa shekaru 91 da kafuwa.

Jaridar wadda ita ce ta fi dadewa a cikin jaridun Najeriya za ta bayar da lambobin yabon ne a babban dakin taro na kasa da kasa dake Abuja babban birnin Najeriya.

Ta ce marigayi shugaba ‘Yar Adua, ya kasance shugaban Najeriya daga ranar 29 ga watan Mayun 2007 zuwa 5 ga watan Mayun 2010, kuma ya bayar da  gagarumar gudun mawa wajen gina Najeriya baki daya.

 

Abdulkarim Rabiu

SHARE

LEAVE A REPLY