Zamfara ta dauki matakan kare lafiya da dukiyoyin maniyyata a sansanin Alhazai

0
149

Hukumar kula da aikin hajji ta jahar Zamfara (Zamfara state Hajj commission) ta dauki kwararan matakan inganta tsaron lafiya da rayukkan maniyyata a sansanin Hukumar dake birnin Gusau.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin kwamishinan Hukumar mai kula da sansanin maniyatan da karbar kudaden hadaya, Alhaji Bello Isah Al-Mufty a zantawarshi da manema labarai a garin Gusau.

Alhaji Bello Isah ya bayyana cewa, bangaren da yake kula da shi a cikin ayyukan hukumar, ya yi ingantaccen tsarin sansanin maniyyatan tare da samar da dukkan wasu muhimman ababen da ake bukata a cikin sansanin.

Ya kuma yi bayani a kan gagarumar nasarar da hukumar ta samu wajen soma jigilar maniyyatan daga jahar zuwa kasa mai tsarki a wannan shekarar.

Haka nan kuma yayi bayani akan tsarin karbar kudaden hadaya daga maniyyatan, domin kawo masu saukin sayen dabbobin hadaya a can kasa mai tsarkin.

 

Ga Hamisu Danjibga dauke da cikakken rahoto:

 

Abdulkarim Rabiu/Hamisu Danjibga

 

LEAVE A REPLY