Hukumar kiyaye haddura ta kasa ta yi gargadi kan tuki cikin maye

Hukumar kiyaye hyaddura ta kasa a Najeriya (FRSC) ta ja kunnen masu ababan hawa da su guji tuki cikin maye domin rage aukuwar haddura a manyan titunan kasar.

 

Shugaban hukuma Mista Boboye Oyeyemi ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar wata kasida mai taken “ci gaban kiyakye haddura ta hanyar tuntuba’’  awani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a birnin Lagos dake kudu maso yammacin Najeriya.

 

A cewar shugaban Hukumar kiyaye hadduran, dokar hukumar ta 2007 da kuma dokar ka’idodin hayya ta 2012, sun haramta tuki cikin maye tare cin tara ko kuma dauri a gidan ga dukkan wanda aka kama ya aikata laifin.

 

Ya ce ’’ yanzu haka an samu raguwar mutanen da suke mutuwa sakamakon aukuwar haddura a kan tituninan  Najeriya da kashi 2.99 cikin 100 na ko wane mutum 100,000 a cikin yawan alummar kasar a shekata 2015, idan aka kwatantan da shekarar 2012 wanda ya yi nuni da cewar 3.61 cikin 100 ne a cikin ko wane mutum 100,000 na yawan alummar kasar ke mutuwa duk shekara’’.

 

Yawan shan barasa da gudun wuce kima na daga cikin musabbain aukuwar haddura a manyan titunan Najeriya.

 

Abdulkarim Rabiu.