Jami’ar Obafemi Awolowo ta bukaci nada mai rikon mukamin shugaban jami’ar.

Kungiyar malaman Jamai’ar Obafemi Awolowo (AOU) dake garin Ile-Ife, ta bukaci shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada mai rikon mukamin Shugaban Jami’ar kafin nadin ainihin wanda zai ja ragamar shugabancin jami’ar.

Mai magana da yawun malaman jami’ar Farfessa Akinola Peter na shashen koyar da lissafi, ya ce nadin mai rokon mukamin shugaban Jami’ar yana da mutukar mahimmancu kwarai domin tabbatar da daidaituwar al’amura a jami’ar yayinda ake ci gaba da fuskantar kalubale.

Muryar Najeriya ta rawaito cewa tun a ranar 30 ga watan Yuni ne Ministan ilimi Adamu Adamu ya sanar da rushe majalisar gudanarwar jami’ar.

Adamu ya kuma bayar da umarnin dakatar da shirye-shiryen nada sabon shugaban Jama’air sai kotu ta kammala bincike.

Da yake gabatar da jawabi ga manema labarai a garin Osogbo babban birnin jihar Osun dake kudancin Najeriya, Farfessa Adegbola ya buakci shugaba Muhammadu Buhari a gudanar da sahihin bincike bisa zargin ta’annati da kudaden jami’ar da ake zargin shugabannin jami’ar da suka gabata suin yi.

Har-ila-yau ya yaba wa gwamnatin Najeriya da ta rushe majalisar gudanarwar Jami’ar.

’’Babu wani malami da zai fito fili karara ya ce ba a saba wa ka’idar aiki ba idan aka yi la’akari da yadda majalisar gudanarwar jami’ar ta gudanar da ayukanta tun daga watan Disambar bara.

’’A ko da yaushe Kungiyar Malaman Jami’a ta kasa ASUU zata nemi gaskiya da adalci wajen nada sabon shugaban Jami’a. Muna fariin ciki kuma munyi amanna da rushe majalisar gudanarwar Jami’ar Obafemi Awolowo, sai dai muna so a nada shugaban riko a kan kari domin kaucewa rashin jagoranci a bangaren shugabancin Jami’ar.’’ In ji Farfessa Adegubola.
Abdulkarim Rabiu.