Jihar Edo: APC ta fitar da jadawalin zaben fidda gwani na takarar gwamna.

Jamiyyar APC mai mulki a Najeriya ta fara shirye-shiyen gudanar da zaben gwamna da ake shirin yi a ranar 10 ga watan Satumba a jihar Edo dake yankin Naija- Delta a Najeriya.

Sakataren shirye-shirye na jam’iyyar APC, Sanata Osita Izunaso yayin da yake zantawa da manema labarai a sakatariyar jam’iyyar dake Abuja babban birnin kasar, ya bayar da cikken bayani akan irin shirye-shiryen da jamiyyar ta yi  kawo yanzu.

“ daga ranar litinin 16 ga watan Mayu zamu fara da taron masu ruwa da tsaki a garin Abuja. Za a fara sayar da fom na neman tsayawa takara a ranar Talata 17 ga wata. Kuma za a ci gaba da sayarwa har 3 ga watan Yunin 2016. Daga ranar 6 ga watan Yuni ana sa ran duka masu sha’awar tsaya wa takara su cika fom su dawo da su hedikwatar jam’iyyar ta kasa dake garin Abuja.

“ za a fara tanatance duka ‘yan takara wadan da suka dawo fom dinsu a ranar laraba 8 ga watan Yuni. Za a a ci gaba da tantancewar har zuwa 12 ga watan Yunin. Idan kuma a ka fuskanci matsaloli a wajen tantanc ewar, kwamitin daukaka kara zai tunkaresu a daga ranar Litinin, 13 zuwa 15 ga watan yuni.

“za a gudanar da zaben fidda gwanin na takarar Gwamna a birnin Benin ranar Asabar 18 ga watan Yunin 2016. kwamitin daukaka kara zai yi zamansa a tsakanin ranar litini 20 da 23 ga watan Yunin 2016.

“za a sayar da fom din nuna sha’awar takara akan Naira dubu dari bayar, yayin da kuma za a sayar  fam din tsaya wa takarar akan Naira Miliyan biyar.

“Mata masu sha’awar takara ba za su biya kudin fom ba, kyauta muke bai wa mata fom a jamiyyar APC. in ji

A watan Satumba mai zuwa ne dai idan Allah ya kai mu a ke sa ran wa’adin mulkil Gwamna Adams Oshiomole wanda shi ma dan jamaiyyar APC ne zai kare.

 

 

 

Abdulkarim Rabiu