Jihar Kano ta jaddada kudirinta na kawar da Polio

Gwamnatin jihar Kano dake arewa maso yammacin Najeriya ta jaddada kudirinta na kawar da cutar shan inna wato Polio daga cikin birnin kanon dabo, duk kuwa da matsalar karancin kudaden shiga sakamakon faduwar fashin danyen mai a kasuwar duniya.

 

Gwamnan jihar kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a wajen sake kaddamar da shirin rigakafin cutar na tsakiyar shekaran nan da muke ciki wanda ya gudana a jihar.

 

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya gudanar tare da shugaban gidauniyar Bill da Melinda Gates da kuma shugaban kamfanin Rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji aliko Dangute.

 

Gwamna Ganduje ya sha alwashin ci gaba da jagorancin shirin da ma sauran shirye-shirye na ci gaban al’umma.

 

‘’ mun yi garanbawul a hukumar samar da kudaden shiga ta jiha ta yadda zata rage dogaro da kudaden da muke samu daga gwamnatin tarayya kuma muna ci gaba da kokarinmu na kawar da cutar shan inna’’ in ji Gwmna Ganduje.

 

Domin tabbatar da gudanar aikin tattara bayanai da sauran ayyukan wayar da kan jama’a agame da cutar Polio suna tafiya yadda ya kamata, gwamnan ya bayar da tabbacin cewa a wannan karon shi da kansa zai tabbatar da ganin an gudanar da rigakafin a duk fadin jihar.

Har-ila-yau Ganduje ya bayyana godiyarsa ga Masarautar Kano, da ma duk sauran masu ruwa da tsaki dangane da kokarin da suke yi na kawar da cutar ta Polio.

 

Abdulkarim Rabiu.