Jihar Kano ta ware Naira miliyan 115 don tallafawa dalibai dake karatu a kasashen waje

Gwamnatin jihar Kano dake arewa maso yammacin Najeriya ta amince a ware Naira Miliyan 155, da dubu 477 domin biyan alawus alawus ga daliban jihar 459 da suke karatu a kasashe shida daban-daban dake fadin duniya.

Daliban dai na cikin tsarin bayar da tallafin karatu na gwamnatin jihar, kuma suna karatun digiri na daya da na biyu a jami’oin dake kasashen China, da Inda, da Cyprus, da Masar, da Uganda da kuma Sudan.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Kwamared Muhammad Garba ne ya sanar da hakan yayin da yake yi wa manema labarai jawabi akan abin da aka tattauna a taron majalisar zartarwar jihar karo na 52.

Yace majalisar ta amince a ware Naira Miliyan 138 domin biyan bashin kudin makarantar dalibai 89 da gwamnatin da ta gabata ta dauki nauyin karantusu a wata jami’ar koyun tukin jirgin sama dake kasar Jordan.

Kazalika a cewar Kwanmared Garba majalisar ta amince da ware Naira Miliyan 389.3 domin daukar nauyin karatun daliban jihar 377 a jami’ar fasaha ta Bells, dake garin Otta a jihar Ogun daga shekarar karatu ta 2014-2015 da kuma 2015-2016.

Kwamared Muhammad Garba ya kara da cewa za a ware wa kwalejin Fasaha ta jihar Kano Naira Miliyan 120 domin daukar dawainiyar ziyarar da hukumar kula da ilimin kerekere zata kawo domin tantattancewa tare da tabbatar da ingancin kwasakwasai 51 da ake koyar wa a kwalejin, wadanda tun daga shekara ta 2012 ba a tantancewasu ba.

Sauran kudaden da aka ware a taron sun hada da Naira miliyan12.9 da aka ware wa shirin kula da lafiyar iyali na kasa da kasa domin ci gaba da gudanar da shirin yaki da cutar kanjamau wato HIV/ AIDS mai karya garkuwar jiki, da kuma Naira Miliyan 28, 025,347 domin gina karamar tashar kashe gobara a kasuwar Muhammadu Abubakar Rimi.

 

Abdulkarim Rabiu