Kakakin Majalisar wakilai ya bukaci Musulmai su yi amfani da koyar watan Ramadan.

Kakakin majalisar dokokin Najeriya Mista Yakubu Dogara ya bukaci al’ummar Musulmi da su yi amfani kyawawan dabi’un da suka koya a lokacin azumin watan Ramadan da aka shafe kwanaki talatin ana yi.

A sakonsa na Sallah Karama ga al’ummar Najeriya, Mista Dogara ya bayyana cewar Watan Azumi mai tsarki ya bai wa Musulmai damar nuna kauna da tausayi da kirki a tsakanin jama’a adon haka ya shawarce su da su ci gaba da tausaya wa sauraran jama’a ko da kuwa bayan watan Ramadan din ne.

Wata sanarwa da aka fitar a Abuja babban birnin tarayyar kasar, ta bukaci al’ummar Musulmi da su yi amfani da Sallah karamar wajen yi wa Najeriya addua domin shawo kan matsalonlin da take fuskanta.

‘’ bari in yi amfani da wannan dama domin bukatar mabiya addinin Musulci su yi amfani da lokacin Bikin sallah Karama domin amfani da darrusan da suka koya a cikin watan Ramadan kana su ci gaba da amfani dasu a rayuwarsu ta yau da kullum, wadanda suka hada da rashin son kai, sadaukar da kai, hakuri, kawar da kai da imani’’. In ji Dogara.

Har-wa-yau kakakin Majalisar wakilan ya bukaci a yiwa kasa addu’ar samun nasara, da kariya, da kuma ikon cimma burin da shugaba Muhammadu Buhari ya daukarwa al’ummar Najeriya.

Abdulkarim Rabiu.