Kungiyar Sunturi ta Najeriya ta bukaci karin tallafi a ayyukanta na tabbatar da tsaro

Kungiyar Sunturi ta kasa a Najeriya wato (Vigilante Group Of Nigeria) a turance, ta bukaci dukkannin matakan gwamnati da ma sauran daidaikun jama’a musamman masu hannu da shuni da kuma masu fada aji da su rika taimaka mata a kokarin da ta ke yi ta tabbatar da tsaro a cikin kasar.

 

Shugaban kungiyar, Kwamanda Janar Usman Muhammad Jahun, ne ya bukaci hakan yayin da yake zantawa da wakilin Muryar Najeriya a ofishinsa dake a Abuja babban birnin Najeriya.

 

Kwamanda Janar Usman yace Kungiyar sunturi tana bayar gaggarumar gudunmawa wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Najeriya, musamman a yankunan da suke fama da kalubalen tsaro.

 

Ya ce kungiyarsa tana taimaka wa jami’an tsaro da suka hada da sojoji da ‘yansanda a duka yankunan da ke fama da matsalar tsaro musamman yankin arewa maso gabas dake fama da rikicin Boko Haram da ma duka sauran yankunan kasar dake fuskantar kalubalen tsaro.

 

Shugaban kungiyar suntrin ya ce kungiyarsa tana taimakawa sojoji da yansanda ayyukan suntrin da suke yi a yankunan da suke fama da bayarin shanu, da yan fashi da makami da kuma rikicin makiyaya da manoma, kana da kama ‘yan daba da kungiyoyin matsafa.

 

To sai dai duk da irin kokarin da suke yi na taimaka wa jami’in tsaro, tallafin da suke samu baya isar su gudanar da wasu ayyukansu, ganin cewa ita kungiya ce ta ayyukan sa kai, bata da wata takamaimiyar hanyar samun kudaden shiga, adon haka ya yi kira ga gwamnati da sauran jama’a da su rika tallafa musu.

 

“taimakon da muke nema ba lalle ne sai na kudi, mutun yana iya sayan kayan aiki, ko da tocila ko batir ne ya bai wa kungiyar sunturi ta unguwarsu, adon haka muna kira ga gwamnatoci da kanfanoni masu zaman kansu da ma sauran daidaikun jama’a da su rika tallafawa wannan runduna ta mu’ In ji Kwamada Janar Usman.

 

Kazalika shugaban kungiyar sunturin ya kuma yaba wa jihohin da suke taimakawa kungiyar musamma ma wadanda suka bayar da gudunmawar motoci da kayan aiki, da kuma biyan alawus ga ‘yan kungiyar, kana da wadanda suka yi dokoki.

 

Sannan ya yi kira ga wadanda basa taikamawa da suka hada da wasu jihohi da kananan hukumi da masu rike da mukamin siyasa da kuma masu hannu da shuni da su yunkura, su tabbatar sun tallafa wa kungiyar a duka matakan gwamnati uku.

 

 

Abdulkarim Rabiu